Isa ga babban shafi
Najeriya

Amnesty da UNICEF sun bukaci a kare rayukan yara a Najeriya

Kungiyar Kare Hakkin Bil Adama ta Amnesty International, tare da Hukumar kula da ilimin yara ta Majalisar Dinkin Duniya, sun ce ya zama wajibi ga hukumomin Najeriya su kare lafiyar yara da kuma hakkinsu na samun ilimi.

Wasu dalibai a wata Makaranta da ta ci wuta a garin Maiduguri
Wasu dalibai a wata Makaranta da ta ci wuta a garin Maiduguri AFP
Talla

Mataimakiyar Daraktan Kungiyar Amnesty, Lucy Freeman ta koka kan harin da aka kai Yobe wanda ya hallaka dalibai 22 da malaminsu guda, inda ta bukaci gudanar da bincike da hukunta wadanda suka aikata aika aikan.

Daraktan Hukumar UNICEF mai kula da Afrika ta yamma da Afrika ta tsakiya, Manuel Fontain, yace babu wani hujja na kai wa yaran makaranta irin wannan mummunar harin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.