Isa ga babban shafi
Najeriya

Gwamnatin Najeriya na hasarar Ganga dubu 400 ta danyen Man Fetir kowace Rana

Yanzu haka dai hukumomin Najeriya sun nuna cewar tattalin arzikin kasar na cikin halin kila-wa-kala na rashin sanin makomar sa, sakamakon yanda Najeriyar ke hasarar Gangar danyen Mai dubu 400 kowace Rana ta Allah, saboda yanda masu satar Danyen Man ke cin Karen su babu babbaka.

Motocin dakon mai a Najeriya
Motocin dakon mai a Najeriya Channels tv
Talla

Wannan dai yayi sanadin fitar da bayannan cewar sashen tattara Harajin kasar ta Najeriya na fuskantar koma-baya, a dai dai lokacin da ake dari-darin cewar gwamnatin kasar ba zata iya aiwatar da tsarin kasafin Kudin tan a wannan shekarar ba.

Ministar Kudi ta kasar Mrs Ngozi Okonjo Iwela wadda ta bayyana a gaban kwamitin Majalisar wakilai ta kasar mai kula da tsarin kasafin Kudi, domin karba gayyatar da kwamitin ya yi mata ta bayyana cewar an samu rangwame ga Harajin da Najeriya ke Tarawa.

Sai dai Ministar ta ce Gwamnatin Najeriya ta kafa sashe na musamman da zai hukunta masu satar danyan man fetur a kasar.

Wannan dai ya zo ne kwanaki kadan bayan da ministar kudi Ngozi Okonjo Iweala ta sanar da cewa kasar na asarar Naira bilyan 150 a kowane wata sakamakon satar mai da ake yi.
Shi dai wannan sashe yana a karkashin jagorancin Mohammed Adoke ne wato ministan ma’aikatar shari’a na kasar, kuma akwai dokokin da suka tanadi hukunta masu aikata irin wannan laifi na akalla tsawon shekaru 21 a gidan yari.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.