Isa ga babban shafi
Najeriya

Kungiyar MEND ta yi barazanar kai wa Musulmin Najeriya hare hare

Kungiyar MEND da ke ikirarin fafutikar 'Yantar da yankin Niger Delta a Najeriya ta aikawa Kafofin yada labarai sakon gargadin kaddamar da hare hare ga Masallatai da cibiyoyin addini da kuma manyan Malaman addinin Islama a ranar 31 ga watan Mayu. Kungiyar tace wannan wani martani ne a madadin mabiya Addinin Kirista.

Des membres du Mouvement d'émancipation du Delta du Niger (MEND).
Des membres du Mouvement d'émancipation du Delta du Niger (MEND). AFP/PIUS UTOMI EKPEI
Talla

“Hare haren da zamu kai a Masallatai da sansanin aikin Hajji da cibiyoyin addini da taron musulunci da kuma kisan manyan malaman addinin Islama da ke yada fatawar la’anta, shi ne babban manufar wannan fafutika mai suna Operation Barbarossa” inji sanarwar da kungiyar ta aiko.

Sanarwar ta ce za ta aiwatar da wannan manufar ce da sunan wakilcin Kiristocin Najeriya, kuma babu mai iya hana ta kaddamar da wadannan hare-haren illa Kungiyar Kiristoci ta kasar CAN, da Cocin Katolika, da kuma shugaban kungiyar da ke tsare Henry Okah a kasar Afrika ta Kudu.

Kungiyar ta ce za ta yi hakan ne a matsayin mayar da martani a game da hare haren da ake dangantawa da kungiyar Boko Haram a kan wuraren ibadar Kirista, kuma dakatar da kai wa wuraren hari ne kawai zai sa MEND ta dakatar da aiwatar da wannan barazanar.

Daga karshe sanarwar ta MEND ta ce ba ruwanta da irin hare haren da ake kai wa gidajen yari da dai sauran wurare saboda hakan ba su shafi manufofin kungiyar ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.