Isa ga babban shafi
Masar

‘Yan Uwa Musulmi za su ci gaba da zanga-zanga bayan samun hasarar rayuka a Masar

Akalla mutane 24 ne suka mutu a sassan yankunan kasar Masar a ranar Juma’a a zanga-zangar karo da juna tsakanin magoya bayan hambararren Shugaban kasa da kuma ‘Yan adawa. Rikicin tsakanin bangarorin biyu ya barke ne bayan da jami’an tsaro suka bindige wasu magoya bayan Morsi guda uku.

Arangana tsakanin 'Yan adawa da magoya bayan Shugaba Mohammed Morsi da Sojoji suka hambarar a saman madafan ikon Masar
Arangana tsakanin 'Yan adawa da magoya bayan Shugaba Mohammed Morsi da Sojoji suka hambarar a saman madafan ikon Masar REUTERS/Asmaa Waguih
Talla

A birnin Alexandria an samu mutuwar mutane kimanin 12 kuma mutane 200 ne suka samu rauni, a birnin Al Kahira mutane biyar ne aka ruwaito sun mutu.

A garin El Arish, ‘Yan sanda biyar ne suka mutu, sai dai babu tabbaci ko wadanda suka kashe ‘Yan sandan masu adawa da juyin mulkin da sojoji suka yi wa Shugaba Morsi ne.

Dubban magoya bayan Jam’iyyar ‘Yan uwa Musulmi ne suka fito saman tituna a sassan yankunan Masar bayan kammala sallar Juma’a domin la’antar abin da suka kira juyin Mulki da Sojoji suka yi wa Mohammed Morsi.

Ana sa ran sabuwar gwamnatin Rikon kwarya ta babban alkali Mansur Adly za ta bayyana sunan sabon Firaminista.

A ranar Laraba ne Sojoji suka tumbuke Mohammed Morsi, shugaba na farko da aka zaba a Masar bayan kawo karshen mulkin shekaru sama da 30 na Hosni Mubarak.

A ranar Assabar, magoya bayan Jam’iyyar ‘Yan uwa Musulmi ta Mohammed Morsi sun sha alwashin ci gaba da zanga-zanga domin neman Sojoji su dawo da gwamnatin Morsi  da al’ummar kasa suka zaba.

Sai dai akwai dubban ‘Yan adawa da suka kwashe dare a dandalin Tahrir a birnin Al Kahira.

Akwai arangama da aka yi tsakanin masu goyon bayan Morsi da kuma ‘Yan adawa a saman gadar da ake kira Octoba inda bangarorin biyu suka kona tayu tare da amfani da duk abinda ya sawwaka suna jifar juna.

Rikicin Masar dai ja hankalin aminanta na kasashen Yammaci da Amurka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.