Isa ga babban shafi
Masar

Sojin Masar sun hambarar da gwamnatin Morsi

Babban Kwamandan Sojin Masar Janar al Sisi ya hambarar da gwamnatin Shugaba Morsi tare da nada babban alkalin kotun Koli a matsayin shugaban rikon kwarya wanda zai jagoranci gaggauta gudanar da sabon zaben shugaban kasa.

Babban Hafsan Sojin Masar Abdel Fattah al-Sisi
Babban Hafsan Sojin Masar Abdel Fattah al-Sisi REUTERS/Stringer
Talla

Sojojin sun dakatar da kundin tsarin mulki tare da bayyana bukatar kafa sabuwar gwamnatin kwararru ta ‘Yan boko zalla. Dubban masu adawa da gwamnatin Morsi ne suka barke da murna bayan Soji sun bayyana daukar matakin.

Janar Abdul Fattah al-Sisi yace sun amsa kiran Mutanen Misrawa ne domin kare juyin juya halin da suka yi na tabbatar da mulkin demokradiya.

Wani babban na hannun damar Shugaba Morsi ya bukaci magoya bayan shi da daukacin al’umar Masar su kai zuciya nesa domin samun zaman lafiya kamar yadda ya ke shaidawa Kamfanin Dillacin Labaran Faransa.

Tuni dai Sojojin suka ba Gwamnatin Morsi wa’adin sa’o’I 48 don amsa kiran ‘Yan kasa. Amma magoya bayan shugaban suna ganin babu adalci domin sun linka yawan ‘Yan adawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.