Isa ga babban shafi
Masar

Mutane 74 sun mutu a filin wasan kwallon kafa a Masar

A Kasar Masar, Akalla mutane 74 suka mutu wasunsu kuma da dama suka jikkata sanadiyar wani rikici daya barke a filin wasan kwallon kafa tsakanin abokan hammaya a birnin Port Said. Hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA tace wannan ranar bakin ciki ga kwallon kafa.

Filin wasan kwallon kafar birnin Port said inda rikici ya barke tsakanin magoya bayan kungiyoyin kwallon kafa a kasar Masar
Filin wasan kwallon kafar birnin Port said inda rikici ya barke tsakanin magoya bayan kungiyoyin kwallon kafa a kasar Masar REUTERS/Stringer
Talla

wannan rikicin shi ne irinsa na farko a tarihin kwallon kafa, kuma rikicin ya barke ne bayan fura usul ta karshe da alkalin wasa ya yi inda kungiyar Al Masri ta doke Al Ahly ta Al kahira ci 3-1.

A filin wasan dai an yi musayar duwatsu ne da farfasa kwalabe tsakanin magoya bayan kungiyoyin kwallon kafar guda biyu.

Yanzu haka dai a shafin Internet akwai hutunan dimbim mutane da rikicin ya rutsa dasu jina jina.

Jam’iyyar Musulunci ta Brotherhood ta zargi magoya bayan hambararren shugaban kasar Hosni Mubarak da kitsa rikicin.

Sai dai a yau ne majalisar kasar karkashin jagorancin Fira Minista Kamal Ganzuri, zasu gana domin tattauna wannan rikicin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane 74.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.