Isa ga babban shafi
Brazil

Roberto Carlos zai yi ritaya a watan Disemba

Dan wasan Brazil kuma Roberto Carlos ya tsegunta cewa a watan Disemban bana ne zai yi Ritaya daga Tamola. Carlos mai shekaru 38 yana taka kwallo ne da kuma taimakawa wajen horar da ‘yan wasa a kungiyar Anzhi Makhachkala ta kasar Rasha, amma kwangilar shi da kungiyar zata kawo karshe ne a watan Yunin badi.

Roberto Carlos, dan kasar Brazil
Roberto Carlos, dan kasar Brazil Майоров Владимир
Talla

Carlos ya lashe kofin duniya a 2002 da Brazil tare da lashe kofin Copa America guda biyu a 1997 da 1999.

Carlos ya kwashe tsawon shekaru 11 yana taka kwallo a Real Madrid ta Spain, inda ya lashe kofin zakarun Turai uku da kofin La liga hudu.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.