Isa ga babban shafi
Indiya

An kammala cinikin Crespo da Okocha da Cannavaro a Indiya

A sabuwar gasar kwallon kafa da za’a bude a kasar Indiya inda za’a ba baje tsoffin ‘yan wasa, dan kasar Argentina ne Hernan Crespo ya fi sauran tsoffin ‘yan wasan tsada. An bayyana Crespo zai karbi albashin kudi Dala $840,000 a shekara, a kungiyar Barasat.

Dan wasan kasar Italia Fabio Cannavaro rike da kofin gasar cin kofin Duniya
Dan wasan kasar Italia Fabio Cannavaro rike da kofin gasar cin kofin Duniya Reuters
Talla

Dan kasar Italiya Fabio Canabaro shi ne kungiyar Siliguri zata biya kudi $ 830,000.

Robert Pires dan kasar Faransa shi zai karbi kudin albashi $800,000 a kungiyar Howrah,

Jay Jay Okocha na Najeriya zai karbi albashin kudi $550,000 daga kungiyar Durgapur.

Masu shirya wannan sabuwar gasa a indiya sun ce a farkon watan Fabrairu zasu sanar da ranar fara gasar, amma tun da farko sun bayyana cewa a ranar 25 ga wata ne za’a bude gasar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.