Isa ga babban shafi
Syria-Rasha

Rasha ta jadadda goyan bayan ta ga Syria

Daya daga cikin janarorin Amurka  Joe Dunford ya bayyana cewa jiragen yakin kasashen Amurka,Faransa da Ingila sun kaddamar da farmaki zuwa Syria da misalin karfe daya agogon Amurka, farmakin ya ba su damar lalata  cibiyoyin sarrafa makamai masu guba a harabar Damascus da Homs. 

Shugaban Rasha Vladmir Putin da Shugaban Syria Bashar Al Assad
Shugaban Rasha Vladmir Putin da Shugaban Syria Bashar Al Assad Sputnik/Mikhail Klimentyev/ via REUTERS
Talla

Rasha a kokarin ta na kare muradun gwamnatin Bashar Al Assad ta sanar da kakkabo makamai masu linzami 71 daga cikin makaman da jiragen yakin Amurka,Faransa da Ingila suka harba zuwa wasu bariqin sojojin Syria.

Hukumomin Rasha sun bayyana cewa  makamai 103 ne jiragen yakin kasashen suka harba,yayinda rundunar tsaron Syria tare da hadin gwiwar Rasha suka kakkabo makamai 71.

Shugabanin kasashen Faransa,Amurka da Ingila sun gabatar da jawabai zuwa al'umar kasashen su don kare mataki kai farmaki Syria.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.