Isa ga babban shafi
Syria

Wakilan Majalisar dinkin Duniya za su isa Syria

Sweden ta yada rubutacciyar matsayar da aka cimma a zauren Majalisar dinkin Duniya a kan batun aika wakilan hukumar a Siriya don kawo karshen batun makami mai guba ga baki daya.Bukatar aika wakilan majalisar dinkin Duniyar ta taso ne a wani taron kwamitin tsaro na majalisar dunkin Duniya. 

Taro a zauren Majalisar dinkin Duniya dangane da batun Syria
Taro a zauren Majalisar dinkin Duniya dangane da batun Syria REUTERS/Brendan McDermid
Talla

A cikin sirri dai ne aka gudanar da taron tattaunawar kan barazanar daukar matakin Soji a kan Syria domin koya mata hankali kan zargin da ake mata na amfani da makami mai guba a yankin birnin Dhouma da ke hannun yan tawaye.

Jakadan kasar Sweden Olof Skoog ya ce ya na fatar majalisar dinkin Duniya ta amince da bukatun da ya gabatar dangane da hakan ba tare da wani bata lokaci ba domin lokaci na kurewa, ya na nufin batun fara kai wa Syria farmaki.

Rubutacciyar bukatar dai ta bayyana cikakken goyon baya akan gudanar da aikin neman hakikanin abinda ke faruwa ne a Syria daga wakilan kungiyar nan mai fada da masu karya ka’ida wajen amfani da makami mai guba a Duniya, tare da bukatar shi kashin kansa Sakataren Majalisar dinkin Duniya Antonio Guterres ya kafa ayari mai karfi da zai dakatar da bude wuta tsakanin bangarori biyu masu fada da juna a Syria da kuma warware duk kullaliyar da ke akwai da kuma ke kai Soji ga amfani da makami mai Guba.

An ce dai tsakanin Alhamis da Jumu’a ne ake sa ran wakilan kungiyar nan mai hana amfani da makami mai guba za su isa a Syria domin fara aikinsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.