Isa ga babban shafi
Syria

Ana dakon matakin da Amurka za ta dauka a Syria

Bayan da Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya kasa cimma matsayi na bai-daya dangane da matakin da ya kamata a dauka kan kasar Syria a game da zargin amfani da makami mai guba a yakin da ake yi a Syria, a yanzu dai hankula sun karkata zuwa ga kasar Amurka da kawanyenta domin ganin irin matakin da za su dauka kan gwamnatin Bashar Assad.

Jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya  Nikki Haley ta ce, Amurka da kawayenta za su dauki mataki akan Syria duk da gaza cimma matsaya a zamansu na jiya
Jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya Nikki Haley ta ce, Amurka da kawayenta za su dauki mataki akan Syria duk da gaza cimma matsaya a zamansu na jiya REUTERS/Shannon Stapleton
Talla

A zaman da ya gudanar a yammancin jiya, Kwamitin Tsaron ya gaza cimma matsaya dangane da kudurori biyu mabambanta da Amurka da Rasha suka gabatar a gabansa kan yadda za a tunkari wannan batu.

Kamar dai yadda aka saba, kasashen Amurka da Faransa da kuma Birtaniya sun yi baki guda a matsayinsu na wadanda ke fatan ganin Majalisar Dinkin Duniya ta tura kwararru don gudanar da bincike dangane da zargin amfani da makami mai guba a kasar ta Syria.

Bambancin ra’ayi da ke tsakanin manyan kasashen duniya ya sake bayyana a jiya Talata, bayan da Rasha ta hau kujuerar na-ki domin tabbatar da cewa ba a samar da wani kuduri da zai bai wa kasashen damar aikewa da masu bincike ko kuma daukar wani mataki a kasar ta Syria ba.

To sai dai jakadiyar Amurka a Majalisar Nikki Haley ta ce, rashin samar da kudurin ba zai hana Washington da kawanyenta daukar matakin da suke ganin cewa ya fi dacewa a kan kasar ta Syria ba.

Kafin Kwamitin Tsaron ya gudanar da zamansa a jiya, fadar shugaban Amurka White House ta ce, an zanta ta wayar tarho tsakanin Donald Trump da Theresa May ta Birtaniya da kuma Emmanuel Macron na Faransa, kuma ga alama kasashen uku sun amince da daukar mataki na bai-daya kan kasar ta Syria.

Wannan ne dai karo na 12 da Rasha ke hawan kujerar na ki a game da batun kasar ta Syria.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.