Isa ga babban shafi
Majalisar Dinkin Duniya

Majalisar Dinkin Duniya na tattaunawa kan amfani da makami mai guba a Syria

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya bukaci gwamnatin Syria ta bai wa masu bincike damar shiga yankunan da aka kai hari da makami mai guba damar gudanar da bincike ba tare da wata matsala ba.An jima kadan ne kwamitin Sulhu zai gudanar da taro kan harin, yayin da shugaban Amurka ke shirin bayyana matsayin kasar sa.

Zaman Kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya kan zargin gwamnatin Syria da amfani da makamai masu guba kan 'yan tawaye da fararen hula.
Zaman Kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya kan zargin gwamnatin Syria da amfani da makamai masu guba kan 'yan tawaye da fararen hula. REUTERS
Talla

Tun da farko dai Amurka ce ta bukaci kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya kada kuri'ar amincewa da kafa kwamitin bincike kan amfani da makamai masu guba da aka yi a Syria.

A jiya litinin Rasha ta bayyana rashin amincewa da zargin da ke dorawa gwamnatin Syria laifin harin makaman masu gubar da aka kai a ranar asabar da ta gabata a birnin Douma da ke gabashin Gouta, kamar yadda ita ma gwamnatin Syriya ta yi watsi da zargin cewa ta yi amfani da makaman masu guba kan yan adam

A cewar wani jami'in diflomasiyan Rasha za ta hau kujerar naki a kan kudirin da Amurkan ta gabatar da ya kamata kasashe 15 mambobin kwamitin tsaron na MDD su amince da shi.

Wannan dai shi ne karo na 12 da Rashar ke hawan kujerar naki kan matakan ladabtarwa da kwamitin ke neman dauka a kan kasar Syria tun farkon barkewar rikicin kasar a 2011.

Kudirin da Amurka ta gabatarwa Kwamitin zai duba yiwuwar kafa kwamitin bincike mai zaman kansa karkashin jagorancin Majalisar dangane da amfani da makamai masu guba da ake yi a rikicin Syria.

Komitin dai na da wa'adin shekara guda na gudanar da bincike yayinda kuma za a iya sabunta wa'adin zuwa nan gaba.

Majalisar Dinkin Duniya dai ba ta da wani ofishi da ke kula da irin wannan binciken gano ko an yi amfani da makamai masu gubar.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.