Muna da shedar amfani da makami mai guba a Syria-Macron
Shugaban Faransa Emmanuel Macron y ace, yana da sheda kan cewa, gwamnatin Syria ta kaddamar da harin makami mai guba a garin Douma a karshen makon jiya.
Wallafawa ranar:
Shugaba Macron ya ce, nan da wani lokaci zai yanke shawara kan kai wa Syria hari ko kuma a'a.
Tuni dai wasu bayanai suka nuna cewa, kasashen yammaci na shirye-shiryen kai farmaki da makamai masu linzami a matsayin martani kan zargin gwamnatin Bashar Al Assad da amfani da makamin mai guba a Syria.
Sai dai Rasha da ta kasance babbar aminiyar Syria ta fuskan soji, ta gargadi daukan matakan da ka iya tsananta rikici a kasar.
Shugaban Amurka Donbald Trump a shafinsa na Twitter, ya ce, makamai masu linzami na nan a tafe cikin Syria, amma bai sanar da takamammen lokaci harba su ba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu