Isa ga babban shafi
Rasha

"Rasha na da hannu a harin guba a Birtaniya"

Kasashen Birtaniya da Faransa da Jamus da Amurka sun yi Allah-wadai da harin gubar da aka kai wa tsohon jami’in leken asirin Rasha da ‘yarsa, in da suka ce, babu makawa Rasha ce ke da hannu a harin.

Tsohon jami'in leken asirin Rasha, Sergei Sripal da aka kashe da makami mai guba a Birtaniya
Tsohon jami'in leken asirin Rasha, Sergei Sripal da aka kashe da makami mai guba a Birtaniya Kommersant/Yuri Senatorov via REUTERS
Talla

A cikin wata sanarwar hadin-gwiwa, shugabannin kasashen, sun yi tir da harin da aka kaddamar kan Sergei da ‘yarsa Yulia Skripal a birnin Salisbury na Ingila a ranar 4 ga watan Maris.

Gwamnatin Birtaniya ta bayyana gubar a matsayin wadda wani gungun jami’an Tsohuwar Tarayyar Soviet ya kera da ake kira Novichok, yayin da Birtaniyar ta caccaki Rasha bayan ta yi amfani da gubar a kasar Ingila.

Sanarwar ta bukaci gwamnatin Rasha da ta amsa dukkanin tambayoyin da ke da nasaba da harin, musamman ma wajen bada cikakken bayani kan shirin Novichok ga Hukumar Haramta Amfani da Makami mai Guba ta Duniya.

A karon farko kenan da aka yi amfani da wannan gubar a kasashen Turai tun bayan yakin duniya na biyu, yayin da sanarwar ta ce, hakan tamkar karan- tsaye ne ga dokokin kasa da kasa, sannan kuma barazana ce ga kowa.

A tsakankanin shekarar 1970 da 1980 ne, Tsohuwar Gwamnatin Tarayyar Soviet ta kirkiri gubar ta Novichok wadda ta kunshi hade-haden sinadarai masu kisa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.