Isa ga babban shafi
Afghanistan

Mutane dubu 10 sun mutu a Afghanistan a 2017

Wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya, ya ce sama da ‘yan kasar Afghanistan dubu 10 suka hallaka a shekarar 2017 da ta gabata. Rahotan ya kuma yi hasashen mai yiwuwa shekarar 2018 da muka shiga ta fi ta bara muni dangane da hasarar rayukan.

Hare-haren bakin wake sun fin salwantar rayukan jama'a a Afghanistan
Hare-haren bakin wake sun fin salwantar rayukan jama'a a Afghanistan REUTERS/Mohammad Shoib
Talla

Rahoton ya ce an samu mafi akasarin salwantar rayukan fararen hular ne a dalilin hare-haren ‘yan bindiga da kunar bakin wake da ake kai wa wuraren da ke samun cinkoson al’umma a biranen kasar ta Afghanistan.

Mutane 605 suka mutu sakamakon hare-haren kunar bakin wake, yayin da dubu 1da 690 suka jikkata.

Sai dai duk da cewa rahoton ya bayyana 2017 a matsayin wadda aka fi samun hasarar rayukan fararen hula, rahoton na Majalisar Dinkin Duniyar ya bayyana fargabar cewa mai yiwuwa shekarar 2018 da muka shiga ta fi muni idan aka kwatantata da 2017 nan gaba.

Najmuddin Helal, daraktan wata cibiyar kwararrun likitoci a kungiyar Red Cross da ke Kabul, ya ce akalla mutane  dubu 1 da 500 suke karba duk shekara kuma kashi 80 ana yanke musu kafafu ne ko hannaye, wadanda kuma a halin yanzu mafi akasarin ke cikin muwuyacin hali na matsin rayuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.