Isa ga babban shafi
Afghanistan

Sojin afghanistan 15 sun mutu a harin kunar bakin wake

Akalla jami’an sojin Afganistan 15 suka mutu a wani sabon harin kunar bakin wake da aka kai sansaninsu da ke birnin Kabul da tsakar ranar yau Asabar.Wannan dai shi ne hari na biyu da aka kai birnin na Kabul cikin kasa da sa’o’I 24, haka zalika shi ne hari na 7 da aka kai daga ranar Talata zuwa yau Asabar wanda ya hallaka jumullar mutane akalla 200 baya ga jikkata daruruwa.

Wasu mutane kenan da ke duba masallacin da aka kaddamar da harin kunar bakin wake a Kabul babban birnin Afghanistan.
Wasu mutane kenan da ke duba masallacin da aka kaddamar da harin kunar bakin wake a Kabul babban birnin Afghanistan. ©REUTERS/Omar Sobhani
Talla

Ko a jiya ma, harin da aka kai masallacin mabiya shi’a a birnin ya hallaka mutum 56 tare da jikkata 55 wanda kuma tuni kungiyar IS ta dauki alhakin kai wa.

Duk da cewa harin yanzu babu kungiyar da ta dauki alhakin kai wa amma kungiyar Taliban da yi kaurin suna wajen kai hare-aren kan sansanin Jami’an tsaro inda ta dauki alhakin kai hudu daga cikin hare-haren da aka kai cikin makon nan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.