Isa ga babban shafi
Amurka

Trump na fargaban tafka makudi a zaben Amurka

Dan takarar shugabancin Amurka karkashin jam’iyyar Republican Donald Trump ya jaddada kofarinsa na cewa, za a tabka magudi a zaben kasar mai zuwa kuma wannan na zuwa ne bayan kuri’ar jin ra’ayoyin jama’a ta nuna yadda ya ke rasa magoya baya. 

Dan takarar Republican  Donald Trump
Dan takarar Republican Donald Trump REUTERS/Jonathan Ernst
Talla

A karshen makon nan ne, attajirin dan takarar  ya caccaki abokiyar hamayyarsa ta Democrat Hillary Clinton da kuma kafafan yada labarai a dai dai lokacin da ya rage makwanni uku a gudanar da zaben kasar ta Amurka.

Trump ya ce, an kammala kada kuri’a amma sai dai ya rasa samun kuri’u masu yawa daga bangaren mata saboda wata makarkashiya da aka shirya masa wadda ba a taba ganin irinta ba, yayin da ya zargi kafafan yada labarai da tafka makudin.

Wasu masharhanta sun bayyana fargaba kan kalaman Trump, in da suke ce, matuakar ya ci ga ba da korafi, to lallai da yiwuar magoya bayansa su haifar da rikici da zaran ya fadi zaben na ranar 12 ga watan Nuwamba.

Bayan kammala muhawar farko tsakaninsa da Clinton Mr Trump ya ce, zai amince da sakamakon zaben amma daga bisani ya janye wannan maganar a hirar da ya yi da jaridar New York Times, in da ya ce, za su zura idanu don ganin yadda za ta kaya.

To sai dai mataimakinsa Mike Pence cewa ya yi, za su amince da shan kayi matukar haka Amurkawa suka zaba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.