Isa ga babban shafi
Amurka

A gudanar da gwajin shan kwaya kafin mahawara inji Trump

Dan takarar kujerar shugaban kasar Amurka  karkashin jam’iyyar Republican Donald Trump ya bukaci a yiwa shi da abokiyar takararsa Hillary Clinton gwaji na shan kwayoyi kafin a gudanar da mahawarar karshe.

Donald Trump na jam'iyyar Republican da Missis Hillary Clinton ta Democrat.
Donald Trump na jam'iyyar Republican da Missis Hillary Clinton ta Democrat. REUTERS/Lucy Nicholson
Talla

Trump dai ya zargi Misis Clinton ne da shan kwaya a yayin mahawararsu ta karshe da suka yi sai dai bai yi Karin bayani kan irin kwayar ko wata hujja dake tabbatar da hakan ba.

Mr Trump dai na ci gaba da fuskantar suka bayan mata fiye da hudu sun fito a mako guda inda suka bayyana takaici kan cin zarafinsu da ya yi.

A ranar laraba mai zuwa ‘yan takarar biyu zasu gudanar da mahawararsu ta karshe a Las Vegas.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.