Isa ga babban shafi
Amurka

Trump ya nemi gafara kan lalata da Mata

Dan takarar shugabancin Amurka a Jam’iyyar Republican Donald Trump ya nemi gafara sakamakon wani hoton bidiyo da aka fitar da ya nuna attajirin yana furta wasu kalaman batsa na rayuwar shi ta lalata da Mata.

Dan takarar Jam'iyyar Republican a zaben Amurka Donald Trump
Dan takarar Jam'iyyar Republican a zaben Amurka Donald Trump Reuters/Handout
Talla

A cikin bidiyon wanda aka dauka a 2005 kuma jaridar Washington Post ta fallasa a jiya juma’a, Trump ya fadi cewa ya taba kokarin sumbatar wata matar aure tare da kuma fadar dubarun da ya ke bi idan yana son yin lalata da mace.

Hoton bidiyon dai ya janyo wa Trump suka musamman daga bangaren jam’iyyarsa ta Republican, inda wasu suka bukaci dan takarar ya yi murabus.

Sai dai kuma Trump ya fito ya nemi gafara a wani jawabinsa da aka yada ta kafar telebijin a yau Asabar.

Trump ya ce ya yi nadama da kuskure kuma yana neman gafara, tare da alkawalin cewa zai zama mutum nagari.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.