Isa ga babban shafi
Amurka

Hillary da Trump sun tafka mahawarar farko mai zafi

'Yan Takaran shugabancin Amurka, Hillary Clinton da Donald Trump sun tafka mahawarar su ta farko kan zaben shugaban kasar inda suka dinga zargin juna kan manufofin su ga Amurkawa.

Hillary Clinton da Donald Trump sun fafata a Mahawara mai zafi
Hillary Clinton da Donald Trump sun fafata a Mahawara mai zafi REUTERS/Carlos Barria
Talla

Trump ya ce Clinton ba ta da koshin lafiyar da za ta rike mukamin shugaban kasa, inda ya zarge ta da taimakawa wajen rasa ayyukan yi da kuma jefa Amurka cikin hadari.

Ita kuwa Clinton ta zargi Trump da kin bayyana takardun sa na biyan haraji da ya bai wa Shugabancin Vladimir Putin na Rasha da kuma manufar sa kan kasashen da ke kawance da Amurka.

Wakilinmu Yakubu Lukman na dauke da Rahoto daga birnin New York.

01:42

Hillary da Trump sun tafka Muhawara mai zafi

Umaymah Sani Abdulmumin

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.