Isa ga babban shafi
Amurka

Har yanzu Hillary Clinton tana gaban Trump

Yayin da ake tunkarar mahawara ta farko tsakanin ‘yan takarar shugabancin Amurka, bincike ya nuna cewa Hillary Clinton karkashin jam’iyyar Demokrat na kan gaba a samun magoya baya da kashi 4, fiye da abokin Hamayyar ta Donald Trump.

Hillary Clinton tare da abokin hamayyarta Donald Trump
Hillary Clinton tare da abokin hamayyarta Donald Trump REUTERS/Lucy Nicholson (L) and Jim Urquhart
Talla

Kuria’ar jin ra’ayi wasu daga cikin Amurkawa da aka yi tsakanin 16 zuwa 22 ga watan Satumba da muke ciki, ya nuna cewa Hillary Clinton tana da goyon bayan kashi 41, shi kuma Donald Trump karkashin jam’iyyar Republican yake da goyon bayan kashi 37.

Sai dai a iya cewa mai yiwuwa Trump ya kara samun magoya baya ganin cewa mai neman Jam’iyyar Republican ta tsaida shi takarar shugabancin Amurka da ya sha kaye Ted Cruz ya amince ya goyi bayan takarar Donald Trump a neman shugabancin kasar.

Ted Cruz wanda a baya ya nuna zazzafar adawa ga takarar Trump, ya bayyana sauya shawarar da yayi a shafinsa na facebook, inda ya ce Hillary Clinton karkashin Jam’iyyar Republican bata cancanci zama shugabar Amurka ba.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.