Isa ga babban shafi
Amurka

An Nuna Hoton Bidiyo na Donald Trump Na Ashararanci Da Batsa

Dan takaran shugabancin kasar Amurka karkashin jamiyyar Republican Donald Trump ya sake shiga tsaka mai wuya sakamakon wani hoton bidiyo da aka gano an dauke shi a shekara ta 2005, yana ta ashararanci da batsa. 

Dan takaran shugabancin Amurka karkashin jamiyyar Republican Donald Trump
Dan takaran shugabancin Amurka karkashin jamiyyar Republican Donald Trump Reuters
Talla

Jaridar Washington Post  ta wallafa wannan sabon labara da bidiyo, ana sauran wata daya cif-cif a yi zaben kasar Amurkan, kuma ana sauran kwanaki kasa da biyu su sake tafka muhawara tare da ‘yar takaran Amurka karkashin jamiyyar Democrat Uwargida Hillary Clinton.

A martanin sa game da bidiyon, Donald Trump ya roki gafara, domin a cewar sa ya yi da na sani.

Ya ce duk wanda ya san shi ya san cewa irin wadancan kalamai  ba ainihin abin dake cikin zuciyar sa bane.

Ya ce ya nemi gafara da fatan zai iya bakin sa nan gaba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.