Isa ga babban shafi
Amurka

Donald Trump ya lashe zaben fitar da gwani na Republican a Nevada

Dan takarar shugabancin Amurka Donald Trump karkashin tutar jam’iyyar Republican ya lashe zaben fitar da gwani a Nevada da gagarumin rinjaye, fiye da manyan abokan hammayarsa Ted Cruz da Marco Rubio.

Donald Trump, Dan takarar shugaban Amurka a Jam'iyyar Republican
Donald Trump, Dan takarar shugaban Amurka a Jam'iyyar Republican REUTERS/Tami Chappell
Talla

Karo na uku ke nan Trump na samun nasara a zaben fitar da gwani da aka gudanar a Jihohin Amurka. Trump ya zo a matsayi na daya a Jihar New Hampshire da South Carolina, sannan ya zo a matsayi na biyu a zaben Iowa.

Ya samu kashi 42 na kuri’u fiye da Sanata Marco Rubio na Florida da ya zo a matsayi na biyu da kashi 24 da kuma Ted Cruz na Texas a matsayi na uku da kashi 22.

Trump ya godewa ‘Yan republican a Nevada da suka zabe shi a sakon godiya da ya rubuta a Twitter.

Trump ya gode wa mutanen Nevada

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.