Isa ga babban shafi
Amurka

Trump ba zai zama shugaban Amurka ba- Obama

Shugaban Amurka Barack Obama yace Donald Trump dan takarar Jam’iyyar Republican ba zai taba zama shugaban kasa ba. Shugaba Obama ya fadi haka ne a taron manema labarai bayan ya gana da shugabannin kasashen kudancin Asia a California.

Barack Obama ya caccaki Donald Trump na Republican
Barack Obama ya caccaki Donald Trump na Republican REUTERS/Kevin Lamarque
Talla

“Na yi imanin Mista Trump ba zai zama shugaban kasa ba”, inji Obama.

Mista Obama ya ce ya san Amurkawa, sun fahimci mukamin shugaban kasa ba abin wasa ba ne.

“Ba wajen barkwanci ba ne ko kambamawa ko tallata kai”.

Sai dai kuma a lokacin da ya ke mayar da martani, Donald Trump ya ce, abin alfahari ne shugaban kasa ya caccake ka.
Sannan ya ce Obama ya haifar da koma-baya a Amurka.

Trump dai na ci gaba da fuskantar suka daga bangaren abokan hammayyarsa a Jam’iyyar republican da kuma bangaren Democrats.

Wannan musayar kalaman na zuwa ne a yayin da ‘yan takarar neman shugabancin Amurka ke shirin fafatawa a zaben fitar da gwani da za a gudanar nan da kwanaki hudu a jihar South Carolina.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.