Isa ga babban shafi
Amurka

Cruz ya doke Trump a zaben fitar da gwanin Republican a Iowa

Ted Cruz ya samu nasara akan Donald Trump a baganren zaben fitar da gwani na Jam’iyyar Republican da aka gudanar a Iowa a Amurka. A bangaren Democrats Hillary Clinton ta fuskanci kalulabe daga Berni Sanders da suke daf da daf a zaben na Iowa.

Ted Cruz ya doke Trump a Iowa
Ted Cruz ya doke Trump a Iowa REUTERS/Jim Young
Talla

‘Yan Republican sun zabi Cruz ne a matsayin dan takararsu a Iowa, yayin da Trump ya zo a matsayi na biyu da yawan kuri’u fiye da Senata Marco Rubio da ya zo a matsayi na uku.

Ted Cruz ya samu kuri’u sama da kashi 27, yayin da Trump ya samu kashi 24.

Wannan ne karon farko da aka fara zaben fitar da ‘Yan takara a zaben shugaban kasar Amurka da za a gudanar a watan Nuwamba.

A bangaren Jam’iyyar Democrats Hillary Clinton na daf da daf ne da Berni Sanders, inda Clinton ta samu kashi 49.9, Sanders kuma ya samu kashi 49.6.

Nan gaba kuma zasu sake fafatawa ne a New Hampshire.

Ko a zaben baya na fitar da dan takara Clinton ta sha kashi a Iowa a hannun Barack Obama.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.