Isa ga babban shafi
Amurka

Hillary ta fi cancantar zama shugabar Amurka, inji Clinton

Tsohon Shugaban Amurka, Bill Clinton ya yabi matarsa a a matsayin wadda ta fi kowa kwarewa wajen zama shugabar kasar a zaben da za a yi a wannan shekarar ta 2016.

Tsohon Shugaban Amurka Bill Clinton na jawabi a yakin neman zaben Matarsa Hillary Clinton a Nashua
Tsohon Shugaban Amurka Bill Clinton na jawabi a yakin neman zaben Matarsa Hillary Clinton a Nashua REUTERS
Talla

Tsohon shugaban ya bayyana haka ne a wani gangamin da aka yi a New Hampshire, inda ya ke cewar a rayuwarsa a yau babu wani dan takarar da ya fi kwarewa da ilimi da halaye masu kyau da ya zarce Hillary.

Clinton ya ce Hillary ce za ta iya samarwa Amurka ci gaba tsakanin daukacin ‘yan takarar da ke neman kujerar shugabancin Amurka.

Sannan Clinton ya mayar wa da abokin hamayyar Matarsa Donald Trump na Republican da martani kan munanan kalaman da ya ke amfani da su domin caccakarta a yakin neman zabensa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.