Biden ba zai tsaya takarar shugabancin Amurka ba
Mataimakin Shugaban kasar Amurka Joe Biden ya sanar cewa ba zai shiga takarar shugabancin kasar da za a yi a shekarar 2016 ba, abinda ya kawo karshen rade radin da aka dade ana yi.
Wallafawa ranar:
Wannan matakin zai bai wa Hillary Clinton damar ci gaba da jan zarenta a takarar ba tare da wani fitaccen abokin karawa ba.
Daukan matakin na zuwa ne a daidai lokacin da Biden ke juyayin mutuwar dansa mai suna Beau, wanda ya gamu da cutar Kansa a kwakwaluwarsa a watan mayu.
To amma duk da wannan sanarwar, Biden ya ce ba zai yi shiru ba a lokacin yakin nema zabe kuma zai ci gaba da tsoma baki game da makomar Jam’iyyarsa da kasarsa
A na ta bangaren, Clinton ta bayyana Biden a matsayin aboki na gari.
Biden dai ya shafe fiye da shekaru 40 yana harkar siyasa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu