Hillary na gudanar da yakin neman zaben shugabancin Amurka
Tsohuwar sakatariyar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton ta kaddamar da yakin neman zabenta na neman tsayawa takarar shugabancin Amurka a jiya asabar, inda ta ce tana fatar kasancewar mace ta farko da za ta jagoranci kasar a tarihi.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Cliton mai shekaru 67 a duniya, ta ce babbar manufarta ita ce tabbatar da cewa arzikin Amurka ya yadu zuwa ga sauran al’ummar kasar, inda ta bayar da misali dangane da yadda shugabannin kamfanoni 25 kawai, na samun albashin da ya haura na illahirin malaman da ke koyarwa a kananan makarantun kasar.
Cliton dai na fatar tsayawa takarar neman shugabancin Amurka ne a zabe mai zuwa karkashin inuwar jam’iyyar Democrate.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu