Isa ga babban shafi
Najeriya-Amurka

Ziyarar Hillary Clinton a Najeriya

Sakatariyar harakokin wajen Amurka Hillary Clinton ta fara ziyara a Najeriya domin ganawa da Shugaba Goodluck Jonathan bayan Amurka ta saka sunan kungiyar Boko Haram cikin jerin sunayen kungiyoyin ‘Yan Ta’adda na Duniya.

sakatariyar harakokin wajen kasar Amruka, Uwargida Hillary Clinton a ziyarar da ta ke yi a kasashen Afrika
sakatariyar harakokin wajen kasar Amruka, Uwargida Hillary Clinton a ziyarar da ta ke yi a kasashen Afrika
Talla

Tun a ranar 31 ga watan Yuli ne Clinton ke ziyara a Nahiyar Afrika inda ta kai ziyara kasar Senegal da Uganda da Sudan ta Kudu da Kenya da Malawi da Afrika ta Kudu. A yau Alhamis ne kuma ta fara Ziyara a Najeriya kafin ta mika zuwa kasar Ghana da Benin.

Ziyarar Clinton dai wani mataki ne na inganta hulda da kasashen Afrika domin janye hankalin kasashen daga dogaro da kasar China.

Kungiyar kare hakkin Bil’adama ta Human Rights Watch ta bukaci Hillary Clinton tattaunawa da Mahukuntan Najeriya game da daukar mataki akan yadda Sojoji a kasar ke ci gaba da tursasawa Jama’a.

Daniel Bekele babban Jami’in Hukumar HRW yace Najeriya tana fama da rikici da kuma karya doka daga Jami’an tsaro al’amarin da kuma ke barazana ga rayuwar ‘Yan Najeriya.

Hukumar tace akalla mutane 1,400 suka mutu sanadiyar hare haren bama bamai da ake kai wa a Arewacin Najeriya. Kuma Hukumar ta zargi Jami’an tsaro da wuce gona da Iri.

Kafin Ziyarar Clinton, Hukumar HRW tace ta aika wa Jekadiyar ta Amurka da Wasika game da wannan batu.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.