Isa ga babban shafi
Thailand

Maciji Ya Sari Namiji A Mazakutar Sa A Kasar Thailand

Likitoci a wani Asibiti dake kasar Thailand na chan suna ta kokarin ceton rai na wani mutun da maciji  ya sara a kan mazakutan  sa, a lokacin da mutumin ya ke bahaya a masai dake cikin gidan sa.

Fira Ministan Thailand Prayuth Chan-ocha
Fira Ministan Thailand Prayuth Chan-ocha REUTERS/Jorge Silva
Talla

Atthaporn Boonmakchuay, mai shekaru 38, ranga-ranga aka kaishi asibitin Chachoengsao dake gabashin birnin Bangkok.

Ya zuwa wayewar gari  likitoci a Asibitin sun bayyana cewa ya fara gane mutane kuma har yana iya bawali kuma bisa dukkan alamu an kashe radadin cizon da macijin yayi masa a mazakuta.

Matar mutumin ta fadawa manema labarai  cewa da wani guduma ta yi nasaran kashe katon mesan,tare da gudun mawar makwabta, a lokacin da ta ji mijin nata na ta ihu a bahaya, ga mazakutansa a bakin maciji, koina jinni cikin bahayan.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.