Isa ga babban shafi
Thailand

Ana taro kan rikicin bakin haure a Thailand

Wakilai daga kasashe 17 na halartar taron kan rikicin Bakin Haure a birnin Bangkok na Thailand inda dubban mutane yawancinsu ‘Yan kasashen Myanmar da Bangladesh ke ci gaba da ratso teku cikin kwale kwale domin shiga kasashen Malaysia da Indonesia.

Sansanin 'Yan kabilar Rohingya da 'yan Bangladesh da ke kwarorowa  zuwa Malaysia da Indonesia
Sansanin 'Yan kabilar Rohingya da 'yan Bangladesh da ke kwarorowa zuwa Malaysia da Indonesia REUTERS/Soe Zeya Tun
Talla

Taron na kwana guda ne ake gudanarwa a birnin Bangkok na Thailand, kuma wakilan kasashe 17 ne ke tattauna matsalar bakin haure da ke ci gaba da ratso teku zuwa kasashen Malaysia da Indonesia.

Taron na zuwa ne a yayin da Thailand ta kaddamar da farmaki akan masu fataucin bakin haure bayan an gano wani katafaren kabari shakare da gawarwarkin mutane da kasashen Malaysia da Thailand.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce sama da mutane 3,500 suka tsallaka zuwa Thailand da Malaysia da Indonesia, yayin da sama da 2,500 ake hasashen sun makale a teku.

Yawancin mutanen musulman kasar Myanmar ne ‘yan kabilar Rohingya da ‘Yan kasar Bangladesh da ke kauracewa talauci a kasashensu.

Kasashen da rikicin ya shafa ne kuma ke gudanar da taron a Bangkok da suka hada da Thailand da Malaysia da Indonesia da Bangladesh da Myanmar domin tattauna matakan da ya kamata su dauka don magance matsalar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.