Sojojin ruwan Malaysia za su ceto bakin haure
Firaministan Malaysia Najib Razak ya bai wa rundunar sojan ruwan kasar umarnin n ceto wasu kwale kwalen da ke dauke da bakin haure da suka hada da ‘yan kabilar Rohingya daga kasar Myanmar. Cikin sanarwar da ya sanya a shafin shi na Facebook, Najib yace dole a kaucewa hasarar rai, a daidai lokacin da ake fargabar bakin hauren sun makale a kan teku.
Wallafawa ranar:
Hakan na nunayanzu Malaysia za ta shiga aikin neman kwale kwalen bakin hauren da suka bace.
Wannan kuma na zuwa ne a daidai lokacin da wakilai daga Amurka, da sauran kasashen kudu maso gabashin Asiya suka nufi kasar, don tattauna matsalar bakin haure.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu