Isa ga babban shafi
Thailand

An kara kyauta ga wanda ya gano maharin kasar Thailand

Dan hambararen Fraiministan kara Thailand Thaksin Shinawatra ya kara yawan kudin da aka yi alkawarin baiwa dun wanda keda bayanan da zasu taimaka wajen kama mutumin daya kai wani mummunan hari a birnin Bankog.

jami'an tsaro a wurin da aka kai harin birnin Bankok
jami'an tsaro a wurin da aka kai harin birnin Bankok REUTERS/Kerek Wongsa
Talla

Yanzu Panthongtae Shinawatra ya sanya karin Dalar Amurka dubu 200 kan dubu 84 da jami’an tsaron kasar suka sanya kan mutumin daya kai harin na ranar Litinin, inda ya hallaka mutane 20.
Panthongtae, dake rubutu a shafinsa na Facebook, yace mahaifinsa, dake gudun hijira a kasar waje ne, ya bashi umarnin kara kudaden da ake bayarwa.
Harin da aka kaiwa ‘yan asalin kasar China dake yawon bude ido a Thailanm zai iya zama babbar barazana ga harkokin yawon bude, dake samarwa kasar makudadn kudaden shiga a duk shekara.
A halinda ake ciki kuma ‘yan sandan kasar ta Thailand suna ci gaba da nazarin hotunan Bidiyon da ke nuna mutumin da ake zargin shi ya ajiye jikar da Bon din da aka aka harin da shi a wajen yawon bude ido.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.