Sarki Salman na Saudiyya ya kai ziyara Amurka
Shugaban Amurka Barack Obama ya gana da Sarki Salman na Saudi Arabiya, a wata tattaunawar da aka dade ana jira, duk da rashin bin alkibla guda da kasashen nasu ke yi, kan rikicin gabas ta tsakiya.
Wallafawa ranar:
Shugaba Obama, da ya dauki wani mataki na ba sabun ba, inda ya tarbi Sarkin, mai shekaru 79 a duniya, a kofar fadarsa ta White House, ya yaba da tsohuwar abota tsakanin kasashen 2.
Yayin ziyarar ta Sarki Salman a jiya juma’a, shugabannin 2 sun yi alkawarin ci gaba da karfafa dangantaka tsakanin kasashen nasu.
Kasashen Saudi Arabiya da Amurka sun yi hannun rig kan wasu batutuwan da suka shafi gabas ta tsakiya, kama daga rikicin dake faruwa a kasashen Syria da Yemen, sannan kuma da yarjejeniyar Nukiliyan da kasashen yammacin duniya suka kulla da Iran a kwanakin baya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu