Isa ga babban shafi
Yemen-Saudiya

'Yan tawayen Yemen sun kai hari a kan iyakokin kasar Saudi Arabiya

Yau Asabar gamayyar kasashen dake yaki da ‘yan tawayen kasar Yemen karkashin jagoran Saudi Arabia, sun ce mayakan na Huthi sun kai hari a kan iyakokin kasar da Saudiyya. Harin, da yayi sanadiyyar rasa ran mutane da dama, na zuwa ne a daidai lokacin da ake shirin fara taron zaman lafiyan kasar ta Yemen, cikin wannan watan a birnin Geneva.Mayakan na Huthi mabiya Shi’a, dake biyayya ga tsohon shugaba Ali Abdullah Saleh, sun bayyana aniyar halartar taron, na ranar 14 ga wannan watan na Yuni, da ake sa rai zai samar da hanyar kawo karshen rikicin da yayi sanadiyyar rasa ran fiye da mutane 2,000. 

Wasu mayakan Huthi na kasar Yemen
Wasu mayakan Huthi na kasar Yemen ©REUTERS/Khaled Abdullah
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.