Isa ga babban shafi
Yemen-Saudiya

Saudiyya ta kai hari a gidan Ali Abdallah Saleh dake birnin Sanaa

Bayan da suka shafe daren jiya Asabar suna kai hare hare ba kakkautawa, yau Lahadi jiragen yakin kasashen duniya, karkashin jagorancin Saudi Arabiya sun yi ruwan bama bamai a kan gidan tsohon shugaban kasar Yemen Ali Abdullah Saleh. Wani shaidan gani da ido, yace an jefa bama bamai har sau 2 a gidan tsohon shugaban dake tsakiyar birnin Sanaa, sai dai ana ganin Saleh baya Birnin.Ana zargi tsohon shugaban, da goyon bayan mayakan Huthi mabiya shi’a, a rikicin da ‘yan tawayen keyi da hukumomin kasar.Cikin shekarar 2012, Saleh ya saki sakamakon rikice rikicen da kasar ta fada, sakamakon juyin juya halin kasashen Larabawa. 

Tsohon shugaban kasar Yemen, Ali Abdullah Saleh
Tsohon shugaban kasar Yemen, Ali Abdullah Saleh Reuters
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.