Isa ga babban shafi
WHO

WHO ta bukaci kasashen duniya 30 su gaggauta inganta sha’anin kiwon lafiyar su

Hukumar Lafiya Ta Duniya WHO, ta ce kasashen duniya 30 ne ya kamata su gaggauta daukar matakai domin inganta sha’anin kiwon lafiyarsu saboda a halin yanzu ba su da inganci.Hukumar ta ce mafi yawa daga cikin kasashen suna a Afirka ne da kuma Asiya.

REUTERS/Stringer
Talla

Mista Ruediger Krech wani babban jami’i a hukumar ta lafiya ya bayar da misali da kasashen Madagascar, Burundi, Sudan, Afghanistan, Haiti da kuma jamhuriyar Demokoradiyyar Congo acikin wadanda ke fama da matsololin sha'ani kiwon lafiya dake bukatar gyara a cikin gaggawa

Krech dai ya ce, ya zama dole a mayar da hankali kan batun sha’ani kiwon lafiya ba sai annoba ya bulo ba

Hukumar dai ta danganta abin da ya faru a kasashen Guinea, da Liberia da saliyo na cutar Ebola a matsayin darasi

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.