Majalisar Dinkin Duniya
An kaddamar da asusun tara kudade domin yaki da yunwa a Afirka
Majalisar Dinkin Duniya ta kaddamar da gidauniyar Dala bilyan biyu dan taimaka wa mutane miliyan 20 da ke fama da yunwa a nahiyar Afrika.
Wallafawa ranar:
Talla
Shugabar sashen ayyukan jinkai ta Majalisar, Valerie Amos, ta ce adadin mutanen da ke fuskantar barazanar yunwa a nahiyar ya zarce yadda aka saba gani, kuma babu wata kungiya guda da za ta iya magance matsalar.
Amos ta ce kasashen da ke bukatar abincin sun hada da Burkina Faso, Cameroun, Chad, Gambia, Mali, Mauritania, Niger, Nigeria da Senegal.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu