Isa ga babban shafi
Masar

An samu raguwar matsalar karancin abinci-MDD

Majalisar Dinkin duniya tace duk da matsalolin tattalin arzikin da duniya ke fuskanta, amma an samu gagarumar ci gaba wajen cim ma kudirin Majalisar ta fuskar rage yawan masu fama da rashin abinci zuwa rabi, daga shekarar 1990 zuwa shekarar 2015.

Wata Kasuwar Abinci a mazauna Samuel Brahima
Wata Kasuwar Abinci a mazauna Samuel Brahima Laura Angela Bagnetto
Talla

Rahotan da Majalisar Dinkin Duniyar ta fitar, ya nuna cewar an samu gagarumar ci gaba wajen rage yawan masu fama da yunwa a duniya, wanda hakan ke nuna cewar ana iya cim ma muradun karnin ta wannan fannin nan da shekarar 2015.

Rahotan yace tuni aka samu nasarar rage yawan mutanen da ke rayuwa kasa da Dala daya da Centi 25 a rana a shekara 2010, shekaru biyar kafin lokacin da aka tanada.

Rahotan ya kuma bayyana nasarorin da aka samu ta fannin kula da lafiyar al’umma da rage masu kamuwa da cutar kanjamau da rage ma su mutuwa sakamakon cutar cizon sauro da tarin fuka, wanda ya kai ga ceto rayukan mutane miliyan 20.

Sakatare Janar na Majalisar, Ban Ki Moon ya yaba da ci gaban da aka samu, inda ya ke cewar ana samun mata da dama da ke mutuwa wajen haihuwa, yayin da ake da damar magance matsalar.

A karshe rahotan ya bayyana cewar, duk da wadanan nasarori da aka samu, akwai sauran aiki sosai a gaba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.