Isa ga babban shafi
Nijar

Mutane miliyan guda ke fuskantar barazanar karancin abinci

Fira Ministan Jamhuriyar Nijar, Brigi Rafini ya ce al’ummar kasar kusan miliyan guda ne ke fuskantar baraznar karancin abinci, saboda fari da ambaliya da suka shafi wasu sassan kasar.

Shugaban kasar Nijar, Mahamadou Issoufou.
Shugaban kasar Nijar, Mahamadou Issoufou. ©RFI/Delphine Michaud
Talla

Fira Minista Brigi Rafini ya bayyana haka ne lokacin da yake jawabi ga Majalisar kasa, a wani zama na musamman dan amincewa da gwamnatin sa.

Rafini ya ce binciken da suka gudanar ya tabbatar musu da wannan adadi, wadanda ke bukatar ganin an taimaka.

Ya kuma kara da cewa, nan gaba kadan gwamnatin kasar za ta ba da bayanai kan yadda za’a taimakawa mutanen da abin ya shafa nana da watan Disamba, wanda ake sa ran zai ci kudi Dala miliyan 112 da zasu fito daga aljihun gwamnatin kasar da kuma masu bada agaji na kasashen duniya.

Jamhuriyar Nijar na daya daga cikin kasashen dake fama da karancin ruwan sama a Nahiyar Afrika inda fiye da kashi tamanin yankin kasar Hamada ne.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.