Isa ga babban shafi
Nijar

Rafini ya samu amincewar majalisar Nijar

Firaministan kasar Nijar Brigi Rafini, ya samu amincewar Majalisar Dokokin kasar domin ya ci gaba da rike mukaminsa, bayan da ‘yan Majalisar suka jefa kuri’a dangane da hakan a cikin daren jiya.

Mahamadou Issoufou, shugaban kasar Nijar
Mahamadou Issoufou, shugaban kasar Nijar France 24
Talla

Firaministan da ya samu kuri’u 70, yayin da sauran ‘yan Majalisa 47 suka nuna rashin amincewarsu da barin sa domin ci gaba da rike wannan matsayi.

Hakan dai ya zo ne wata daya bayan rugujewar kawancen jam’iyyun siyasar da ya dora Birgi Rafini akan karagar mulkin kasar ta Nijar sakamakon bambancin ra’ayi a tsakanin jam’iyyun siyasar kasar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.