Isa ga babban shafi
Nijar

An gano gawawwakin matafiya 87 a Nijar

Masu aikin agaji a Jamhuriyar Nijar, sun gano gawawwakin matafiya 87 daga cikin mutanen da ke kan hanyar tafiya Algeria daga kasar, kuma a cewar Jami’an agajin mutanen sun mutu ne sakamakon rashin ruwan sha a lokacin da motarsu ta lalace a tsakiyar Sahara.

Yankin Sahara a kasar Libya
Yankin Sahara a kasar Libya galuzzi.it/wikimedia.org
Talla

Almoustapha Alhacen, Jami’in wata Kungiyar agaji ta organisation Aghir In'man, ya tabbatar da adadin gawawwakin mutanen tare da cewa gawawwakin mamatan har sun fara lalacewa, wasu ma har dabbobi sun fara ci.

Kasar Nijar dai mashigi ne da baki ke bi domin tsallakawa zuwa kasashen Arewacin Afrika don samun ayyukan yi.

Gwamnatin Nijar tace yawancinsu mata ne da yara kanana wadanda suka mutu saboda matsanancin kishirwa a yankin Sahara.

Sai dai kuma Wata majiyar tsaro a Nijar tace akwai mutane 21 da suka tsira da ransu cikinsu har da wani mutum wanda ya yi tafiyar tsawon Kilomita 83 zuwa garin Arlit a arewacin kasar.

Majiyar ta kara da cewa akwai mutane 19 da suka samu nasarar tsallakawa zuwa birnin Tamanrasset a kasar Algeria amma an dawo da su zuwa Nijar.

Kasashen Libya da Algeria hanyoyi ne da ke taimakawa Mutanen kasashen yammacin Afrika damar tsallakawa zuwa kasashen Turai

Majalisar Dinkin Duniya tace akalla kimanin mutane 30,000 ne suka keta ta Agadez domin shiga kasashen arewacin Afrika tsakanin watan Maris zuwa watan Agusta a bana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.