Isa ga babban shafi
Nijar

An samu raguwar mutuwar yara Kanana a Nijar

Kungiyar Agaji ta Save the Children, tace Jamhuriyar Nijar ta samu gagarumar nasara wajen rage adadin yara kanana da ke rasa rayukansu a wani bincike da aka yi na shekaru 23. Rahotan da kungiyar agaji ta Save the Children ta bayar, ya nuna cewa Jamhuriyar Nijar na daga cikin kasashe 10 a duniya da suka samu gagarumar nasarar rage yaran da ke mutuwa.

Jerin Mata masu shayarwa a Nijar suna jiran Likita
Jerin Mata masu shayarwa a Nijar suna jiran Likita
Talla

Sauran kasashen sun hada da Liberia da Rwanda da Indonesia da Madagascar da India da China da Masar da Tanzania da Mozambique.

Rahotan kungiyar yace cikin yara 326 daga cikin 1,000 da ke mutuwa a Jamhuriyar Nijar kowacce shekara a 1990 an samu raguwa zuwa 114 a shekarar bara.

Kungiyar ta danganta nasarar da shirin bai wa mata da kananan yara kula kyauta a asibitocin gwamnati.

Wannan binciken an gudanar da shi ne a kasashe 75 na duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.