Isa ga babban shafi
Nijar

Ambaliya ta yi barna a Nijar

Mutane Takwas aka ruwaito sun mutu sakamakon ambaliyar ruwa a garin Maradi da Agadez da Damagaram a Jamhuriyyar Nijar. Mahukuntan kasar sun ce cikin wadanda suka mutu akwai yara kanana guda bakwai yayin da mutane kusan 2,000 suka rasa matsuguninsu.

An samu ambaliyar ruwa a garin Agadez a Nijar
An samu ambaliyar ruwa a garin Agadez a Nijar Raliou Hamed-Assaleh
Talla

Rahotanni sun ce matsalar tafi kamari a Maradi, inda mutane suka samu mafaka a makarantu.

Gidan Rediyon amfani ya ruwaito cewa akwai yara ‘Yan mata guda biyu da suka mutu a garin Damagaran, yayin da kuma a garin Agadez aka samu wata yarinya mai shekaru biyar da ta mutu bayan gini ya rubta da ita sakamakon ambaliyar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.