Isa ga babban shafi
Faransa

Faransawan da aka yi garkuwa da su a Nijar sun isa Paris

Faransawa hudu da aka sako su daga Jamhuriyar Nijar bayan garkuwa da aka yi da su na tsawon shekaru uku sun isa birnin Paris bayan wani jirgin gwamnatin Faransa ya dauko su daga birnin Niamey. 

Lokacin da Faransawan suka sauka a Paris
Lokacin da Faransawan suka sauka a Paris AFP PHOTO/HAMA BOUREIMA
Talla

Jirgin ya bar Nijar ne da sanyin safiyar Laraba dauke da mutanen inda suka samu tarbon shugaba Francois Hollande.

Bayan da suka iso birnin Paris, Shugaban kasa Hollande ya bayyana farin cikinsa tare da girmama mutanen a matsayin wadanda suka kare martabar Faransa.

Da farko rahotanni na nuni da cewa ba a yi amfani da karfin soji ko kuma biyan diyya wajen sako mutanen ba, sai dai bayanan baya-baya nan sun nuna cewa an biya kudin euro miliyan 20 kamin sako Faransawan.

Kamfanin Dillancin labaran Faransa na AFP ya ce a kasar Mali aka samo mutanen lamarin da ya sa Hollande ya mika godiya ta musamman ga kasar Nijar akan irin rawar da ta taka wajen sako 'yan kasarsa.

“Ina so na mika godiya ta ga shugaban Nijar, wanda ya karbo ‘yan kasata.” inji Hollande.

Mutanen da aka sako sun hada da Thierry Dol da Larribe da Pierre Legrand da kuma Marc Feret wadanda aka yi garkuwa da su a ranar 16 ga watan Satumbar shekarar 2010 a wani kamfanin hakar Uranium dake Arlit da ake kira Areva a Arewa maso tsakiyar Nijar.

Matar daya daga cikin wadanda aka sako, Francois Larribe wacce itama aka yi garkuwa da ita a da, aka kuma sako ta daga baya a watan Febrairun shekarar 2011, ta nuna matukar farin cikinta na sako mijinta.

“Wannan abun ne mai sosa rai matuka.” Inji ta.

Shugaban Nijar Mahamadou Issoufou a nashi bangaren ya mika sakon taya murnarshi ga mutanen a lokacin da ya gana da su ya kuma nuna alhinisa game da irin wahalar da suka fuskanta na watanni da dama.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.