Isa ga babban shafi
Nijar

Ministan harkokin wajen Faransa ya gana da shugaban Nijar

Ministan harkokin wajen kasar Faransa Laurent Fabius, wanda ke ganawa da shugaban kasar Nijar Issoufou Mahamadou a birnin Yamai a wannan talata, ya ce akwai bukatar hada gwiwa tsakanin kasar Libya kuma makwabtanta domin fada da ‘yan ta’adda, bayan harin da aka kai wa kasar Nijar a ranar alhamis da ta gabata.

Ministan harkokin wajen Faransa, Laurent Fabius
Ministan harkokin wajen Faransa, Laurent Fabius REUTERS/Anis Mili
Talla

Fabius, ya bayyana wa manema labaran ji kadan bayan ganawarsa da shugaba Issoufou cewa, "akwai matakan da ya kamata a dauka tsakanin Libya da kuma makwabtanta, domin kuwa akwai kungiyoyi na ta’addanci a cikin kasar".

Kamfanin hako makamashin Uranium na kasar Faransa Areva, ya ce harin da ‘yan ta’adda suka kai wa kamfanin da ke garin Arlit na Jamhuriyar Nijar a cikin makon da ya gabata, ba zai gurgunta ayyukan kamfanin a wannan kasa ba.
Shugaban kamfanin na Areva Luc Oursel, wanda ke zantawa da manema labarai a birnin Madrid na kasar Sapin ne ya bayyana haka, inda ya ce sun yi bakin ciki matuka dangane da faruwar wannan hari, da kuma asarar rayukan da aka yi lokacin harin, amma dai kamfanin zai ci gaba da gudanar da ayyukansa kamar yadda ya saba.
A cikin makon da ya gabata ne dai Luc Oursel ya kai ziyara a kasar ta Nijar inda ya gana da shugaba Issoufou Mahamadou, dangane da wannan hari da kuma irin matakan da ya kamata kasar ta Nijar da kumam kamfanin mallakar kasar Faransa su dauka domi tunkarar wannan sabuwar barazana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.