Isa ga babban shafi
Nijar

Shugaban kasar Nijar ya ce 'yan ta'adda na shirin kai hari a Chadi

A yau Litinin Shugaban kasar Nijar, Mahamadou Issoufou ya kai ziyara a garin Agadez domin jajantawa 'yan uwan sojojin da aka kai wa harin kunar bakin wake a cikin wani barikin soja da ke birnin da kuma wasu jami'an tsaron da ke aiki a kamfanin hako uranium na Areva mallakin Faransa, hare-haren da suka yi sanadin mutuwar mutane 33.

Shugaban kasar Jamhuriyar Nijar, Mahamadou Issoufou
Shugaban kasar Jamhuriyar Nijar, Mahamadou Issoufou Laura-Angela Bagnetto
Talla

A lokacin wannan ziyara, shugaban na Nijar ya ce bisa ga dukkan alamu, kungiyar da ta kai harin na garin Agadez, na shirin kai makamancinsa ne a kasar Chadi mai makwabtaka da Jamhuriyar ta Nijar.

A ranar asabar da ta gabata, shugaba Issoufou Mahamadou, jim kadan bayan ganawarsa da shugaban kamfanin hako uranium na Areva wanda ya ziyarce shi a ofishinshi da ke birnin Yamai, ya bayyana cewa mayakan da suka kai kai harin, sun samu kwararowa ne zuwa Nijar daga Libya.

Ministan tsaron Nijar Mahamdou Karidjo ya ce suna hada hannu da makwabtan kasashe domin inganta tsaron kan iyakokinsu.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.