Isa ga babban shafi
Nijar

Shugaban Nijar ya ce wadanda suka kai wa kasar hari sun fito ne daga Libya

Shugaban Jamhuriyar Nijar Issoufou Mahamadou, ya ce wadanda suka kai hari akan wani barikin soja da ke Agadez da kuma kamfanin hako Uranium da ke garin Arlit a cikin jihar ta Agadez a ranar alhamis da ta gabata dukkaninsu sun fito ne daga kasar Libya.

Laura-Angela Bagnetto
Talla

Issoufou Mahamadou wanda ke zantawa da gidan rediyo Faransa RFI a yau asabar, ya ce ko shakka babu maharan sun shigo kasar ta Nijar ne daga Libya, kuma a cewarsa, wannan alama ce da ke kara tabbatar da cewa Libya na a matsayin na ci gaba da kasancewa babbar barazana ga sha’anin tsaron kasashen yankin Sahel.
Kalaman na shugaban Jamhuriyar Nijar sun zo ne jim kadan bayan ganawarsa da babban darakta kamfanin hako Uranium na Areva mallakar kasar Faransa Luc Oursel, wanda ke ziyarar aiki yanzu haka a Jamhuriyar ta Nijar.
Alkaluma na baya-bayan nan dai na nuni da cewa mutane 24 ne suka rasa rayukansu sakamakon wadannan hare-hare guda biyu, yayin da aka kashe maharan akalla.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.