Isa ga babban shafi
Nijar

Harin bom ya hallaka mutane a kamfanin Areva dake Nijar

Wani harin bama bamai da aka kai a cikin motoci kan wani kamfanin hakar sandarin Uranium, ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama Jihohin Arlit da Agadez dake Jamhuriyar Nijar. Ministan Tsaron kasar ta Nijar, Mahamadou Karidjo ya tabbata da aukuwar lamarin a yayin da aka kuma kai wani hari kan barikin sojin kasar dake Agadez.  

Shugaban kasar Nijar, Mahamadou Issoufou
Shugaban kasar Nijar, Mahamadou Issoufou Voice of America
Talla

“Wani mutum ne sanye da kayan soji a cikin wata mota ya tayar da bom din.” Inji wani ma’aikacin kamfanin na Areva wanda aka yi abin a kan idonsa.

Rahotanni na nuna cewa, wanda ya kai harin shi kadai ne ya rasa ransa a yayin da kasar Faransa ta ba da tabbacin cewa an samu wadanda suka hallaka a cikin ma’iakatan kamfanin.

Sai dai kasar ta Faransa ba ta ambaci ko mutane nawa ne suka mutu ba.

Wannan kuma shine karo na farko da aka taba samun faruwar irin wannan hari a kasar ta Nijar wacce itama ta aika da dakarunta zuwa kasar Mali domin yakan ‘yan tawaye kasar.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.