Mayakan MUJAO na Mali sun yi ikirarin daukar alhakin kai harin Agadez
Mayakan kungiyar MUJAO masu neman tabbatar da Shari’ar Musulunci a kasar Mali sun yi ikirarin daukar alhakin kai harin da ya kashe mutane kimanin 19 a sansanin Soji da kuma kamfanin Uranium na Faransa a kasar Jamhuriyyar Nijar.
Wallafawa ranar:
“Mun gode Allah, mun kai jerin hare hare guda biyu ga makiyan Addinin Islama a Nijar” a cewar Kakakin kungiyar Abu Walid Sahraoui.
Abu Walid ya shaidawa kamfanin Dillacin Labaran Faransa cewa sun kai harin ne domin mayar wa Nijar da martani game da hadin kan da ta ba Faransa domin yaki da shari’ar Allah a Mali.
Ministan cikin gidan Nijar Abdou Labo ya tabbatar da mutuwar mutane 19 a hare haren da aka kai a Jahar Agadez da suka hada da dakarun Soji 18 da wani farar hula.
Wannan harin dai shi ne na farko da aka kai a Nijar da ke Makwabtaka da Mali. Kuma Nijar ta taimaka da Dakarunta zuwa Mali domin kakkabe ‘yan tawaye da suka karbe ikon Arewacin kasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu